IQNA

Fiye da maziyarta dubu 420 ne suka ziyarci cibiyar kur'ani da ke Madina

22:44 - April 15, 2026
Lambar Labari: 3494817
Iqna - Fiye da maziyarta dubu 420 ne suka kai ziyara a cibiyar kur'ani mai tsarki da ke Madina domin duba nau'oin kwafin kur'ani da aka adana a wurin.

Jaridar Ahwal ta bayar da rahoton cewa, a cikin watanni 4 na farkon shekara ta 2026, iye da maziyarta dubu 420 ne suka kai ziyara a cibiyar kur'ani mai tsarki da ke Madina domin duba nau'oin kwafin kur'ani da aka adana a wannan cibiya.

Rahoton ya yi nuni da cewa, bisa la'akari da cewa Madina wuri ne da ke samun masu ziyara a kowane lokaci daga kasashen duniya, an bude wannan cibiya domin wasu daga abubuwa na tarihi da suka shafi kur'ani.

A kowace rana dubban mutane suke halartar wanann wuri domin ganewa idanunsu abubuwa da aka adana na tarihi da suka shafi tsoffin kur'anai.

Baya ga haka kuma ana nuna wasu daga cikin kayayyakin tarihin tarihin musulunci, wadanda suke da alaka da lokacin manzo da kuma lokuta daban-daban na tarihin musulunci.

 

4346193

captcha