IQNA

An Tattuna Kan Batutuwan Afghanistan Da Corona Tsakanin Zarif Da Takwarorinsa Na Turkiya Da Qatar  

23:55 - April 13, 2020
Lambar Labari: 3484708
Tehran (IQNA) ministocin harkokin wajen kasashen Iran, Qatar da kuma Turkiya sun tattauna ta wayar tarho kan batun halin da ake ciki a Afghanistan da batun ayyukan hadin gwiwa wajen yaki da corona.

Shafin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya sanar da cewa, an gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad da kuma takwarorinsa na Turkiya Jawish Auglo da kuma na Qatar Muhammad Bin Abdulrahman Al Thani.

Ministocin harkokin wajen kasashen uku sun tattauna batun dambarwar siyasar da ake ciki a kasar Afghanistan, da kuma irin rawar da ya kamata su taka wajen ganin an samar da sulhu tsakanin bangarorin siyasar Afghanistan da basa ga maciji da juna.

Haka nan kuma sun tattauna batun matsalar corona, da kuma ayyukan hadin gwiwa da za su iya yi a tsakaninsu domin fuskantar wannan annoba da take yin barazana ga dukkanin al’ummomin duniya.

 

3891364

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Zarif
captcha