Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nilin cewa, masu amfani da harshen Sudan sun yaba da kyakykyawan karatun da wannan makarancin dan kasar Pakistan ya yi.
Sheikh Nurin Muhammad Sediq ya kasance daya daga cikin mashahuran makaratun kasar Sudan a cikin al'ummar kasar nan, ya rasu ne a watan Nuwamban shekarar 2020 bayan wani hadarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta dawowa daga Wadi Halfa.
A cikin bidiyon da aka ambata, wannan makarancin dan kasar Pakistan yana karanta aya ta 15 zuwa ta 24 a cikin suratu Mubaraka Al-Hashr.