IQNA

Babban dakin karatu na  Amir Al-Mu’minin A Najaf

NAJAF (IQNA) – Laburare na jama'a na Imam Amir al-Mu'minin babban dakin karatu ne a birnin Najaf na kasar Iraki.

Marigayi malamin musulmi Alamah Amini ne ya kafa shi a shekarar 1954, dakin karatu ya kunshi bangarori daban-daban kuma kwamitin amintattu ne ke tafiyar da shi.

Yana da dubban litattafai na tarihi da na zamani a fagage daban-daban kamar littafan Musulunci, Alqur'ani, lissafi, da kimiyyar lissafi. Daliban makarantun hauza daga Iran da Iraki da wasu kasashen duniya ne ke ziyartar dakin karatun.