IQNA

Karatun Mahmoud Shahat Anwar a mukamin Bayat

Tehran (IQNA) Mahmoud Shahat Anwar, matashin makaranci dan kasar Masar, ya karanta ayoyin Suratul Al-Ala a ziyarar da ya kai kasar Comoros a kwanan baya.

Wannan fitaccen kuma mashahurin makaranci na kasar Masar ya gudanar da karatu a cikin da'irar kur'ani na wannan kasa a yayin tafiyarsa zuwa Comoros, wanda aka yi a cikin watan Ramadan, wanda ya samu karbuwa da jin dadi daga al’ummar kasar.