'Yan Pakistan sun gudanar da zanga-zangar adawa da wulakanta Al-Qur'ani
ISLAMABAD (IQNA) Mutane da dama ne a Pakistan suka yi zanga-zangar yin tir da keta alfarmar kur’ani.
Dubban 'yan kasar Pakistan ne suka fito kan titunan manyan biranen kasar a ranar 7 ga watan Yuli, 2023, domin yin tir da wani wulakanci da aka yi wa kur'ani mai tsarki a kasar Sweden.