IQNA

Karatun Suratul Fajr da muryar Abdul Basit

Tehran (IQNA) A cikin ruwayoyi daban-daban, ImamaiMa’asumai  (a.s.) sun dangana surar “Fajr” ga Imam Husaini (a.s.); A kan cewa tashin Annabi mai tsira da amincin Allah ya zama tushen rayuwa da motsi a lokacin duhu kamar ketowar alfijir.

A cikin watan Muharram kuma a ranakun zaman juyayin shahidar  Aba Abdullah Al-Hussein (AS), IQNA  ta fitar da karatun suratu Fajr da sautin fitattun mahardata na duniya. A kashi na uku kuma za a ji karatun suratul Fajr cikin muryar Abdul Basit Muhammad Abdul Samad, shahararren makaranci a duniyar Musulunci.