IQNA

Mulkin Mallaka Ta Hanyar Gurbata Kafofin Sadarwar Kasashen Musulmi

21:57 - March 04, 2014
Lambar Labari: 1383073
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin sabbin hanyoyin mulkin mallaka ita ce hanyar gurbata ala'adun mutane ta hanyar kafofin sadarwa tare da cusa musu wasu abubuwa da ba su da alaka da al'adunsu ko addininsu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Burkina Faso Nuel Wedrago ya bayyana cewa daya daga cikin sabbin hanyoyin mulkin mallaka ita ce hanyar gurbata ala'adun mutane ta hanyar kafofin sadarwa tare da cusa musu wasu abubuwa da ba su da alaka da al'adunsu ko addininsu domin nisantar da su daga gare su.
Ya ci gaba da cewa ko shakka babu kasashe 'yan mulkin mallaka suna da bakaken manufofi kan sauran al'ummomin duniya musamman ma dai kasashen da suka yi mulkin mallaka, wadanda suke cewa sun basu 'yancin kai, amma a zahirin gaskiya babu maganar 'yancin kai, domin kuwa har yanzu irin wadannan kasashe suna fama da matsaloli masu tarin yawa da 'yan mulkin mallakar suke haddasa musu kamar dai yadda muka yi ishara da bangare addini da al'adu.
Banbancin mulkin mallaka na yanzu da kuma lokacin da ya gabata ita ce, ada wadannan kasashen suna shigowa da karfin tuwu su mamaye kasashe tare da dora musu abin da suka ga dama, amma yanzu suna dora mutaten ne kana bin da suke so, sai al'ummomi su ci gaba da yin abin da wadannan kasashe suke so, kuma hanya mafi hadari da suke amfani da ita a halin yanzu su ne hanyoui na sadarwa.
1381609

Abubuwan Da Ya Shafa: Burkina Faso
captcha