Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lemaq cewa, kasar Tunisia ta karyata wasu rahotanni da ke cewa maihaifar da fitina tsakanin al’ummar musulmi Yusuf Qardawi zai koma kasar sakamakon matsin lamabar da yake fuskanta daga mahukuntan kasar Qatar sakamakon kalaman batuncin da yake kan wasu kasashen larabawa na yankin musamman ma hadaddiyar daular larabawa da kuma Saudiyya, gami da Bahrain.
Yusuf Qardawi da ke karkashin liyafar masarautar Qatar ya zargi sarakunan kasashen Larabawa musamman Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait da Bahrain da hannu a zubar da jinin al'ummar musulmi ta hanyar amfani da kudade. Qardawi yana cewar hakika ana zubar da jinin al'ummar musulmi da tarin biliyoyin kudaden sarakunan kasashen Larabawa, don haka ya yi kira ga sarakunan Larabawa musamman sarkin Saudiyya Abdullahi bin Abdul-Aziz kan su ji tsoron Allah tare da komawa kan tafarkinsa.
Wannan kira na Sheikh Yusuf Qardawi ya zo ne sakamakon matakan da kasashen Larabawa suka dauka na goyon bayan hambarar da shugaban kasar Masar Muhammad Morsi tare da tallafawa gwamnatin rikon kwaryar Masar da biliyoyin kudade.
A baya dai Sheikh Qardawi ya fitar da fatawar wajabcin goyon bayan Muhammad Morsi tare da haramcin bijire masa, kamar yadda ya siffanta ministan tsaron Masar Abdul-Fatah Sisi da cewa maha'inci ne da yake kashe mata da tsoffi gami da kananan yara.
1394210