IQNA

Cibiyar Azahar Ta Yi Watsi Da Fatawar Qardawi Kan Haramta Zaben Masar

10:08 - May 17, 2014
Lambar Labari: 1407314
Bangaren kasa da kasa, Babban malamin addini mai bayar da fatawa a jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayar da umarnin gudanar da bincike dangane da hudubobin Yusuf Kardawi da makalolinsa da yake tunzura mutane zuwa ga tayar da fitina, tare da yin watsi da fatawarsa ta haramta zaben kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Ahmad Tayyib ya dauki wannan matakin ne tare da amincewar dukkanin malamai mambobi a kwamitin manyan malaman addini na jami’ar Azhar, bayanin ya ci gaba da cewa za a tantance kalaman batunci da tunzura jama’a da nona goyon bayan ta’addanci da Qardawi yake yi ido refe da sunan addini.
A ranar Lahadi da ta gabata ce kwamitin manyan malaman addini na jami’ar Azhar ya sanar da korar Yusuf Qardawi daga wannan kwamiti, sakamakon mummunar rawar da yake takawa wajen haifar da fitina tsakanin al’ummar kasar Masar.
Yusuf Qardawi wanda yanzu haka yake zaune karkashin masarautar Qatar, ya taka gagarumar rawa wajen bayar da fatawoyin kafirta musulmi tare da halasta zubar da jinisu, tare da ruruta wutar rikici a kasashen Libya, Syria da Masar ta hanyar yin amfani da addini daidai da mahanagar masarautar Qatar, fatawar baya-bayan nan dai it ace ta haramta zaben da za a gudanar da a kasar ta Masar.

1406592

Abubuwan Da Ya Shafa: Qardawi
captcha