IQNA

Gwagwarmayar Musulunci Ta Hana Kafuwar Sabuwar Gabas ta Tsakiya

16:55 - May 28, 2014
Lambar Labari: 1411968
Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren Kungiyar Hizbullah ya ce; A duk lokacin da H.k. Isra’ila ta wuce gona da iri akan kasar Lebanon da al’umma za su fuskanci maida martani daga gwagwarmaya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na shafin yanar gizo na talabijin in Almanar cewa, Sayyid Hassan Nasrullah wanda ya yi jawabi dazu a wurin bikin zagoyowar cin nasarar gwagwarmaya akan yahudawan sahayoniya, ya bayyana cewa; Nasarar da aka samu ta korar ‘yan sahaniya ta zama ginshikin samun wasu nasarori masu yawa da su ka biyo baya,kuma ta kawo karshen shirin Amurka da h.k. Isra’ila na kafa sabuwar gabas ta tsakiya.
Sayyid Hassan Nasarallah ya ci gaba da cewa; Nasarar da gwagwarmaya ta samu akan  nasara ce ga dukkanin al’ummar Lebanon da larabawa da musulmi, domin babu wata kungiya da za ta riya cewa nasararta ce ita kadai. Babban magatakardar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ya kuma ce; matukar babu wani kyakkyawan tanadi na tsaron kasar Lebanon  daga gwamnati gwagwarmayar Musulunci za ta ci gaba da kare kasa. Jagoran kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sayyid Hassan nasrullah ya bayyana cewa makircin da aka shirya wa kasar Syria bai ci nasara ba, maimakon haka ma wannan makirci na ci gaba da rushewa.
Jaridar Al-akhbar ta kasar Lebanon ta nakalto daga Sayyid Nasrallah cewa, abin da aka shirya ma kasar Syria tun farko ba shi da wata alaka da neman gudanar da sauye-sauye na siyasa  akasar a kasar, abin da aka shirya makirci ne na rusa kasar saboda matsayar da ta dauka ta kin amincewa da siyasar Amurka a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, da kuma goyon bayan al’ummar palastinu da take da dukaknin karfinta, gami kawancen da take yi da Iran da kuma Hizbullah,  Sayyid Nasrullah ya ce wannan shi ne bababn dalilin haifar da duk wanna  rikici da duniya take gani a Syria.
Dangane da shigar Hizbullah a cikin yakin Syria kuwa Sayyid Nasrullah ya ce dole ne Hizbullah ta yi haka, domin kuwa da ta bata yi hakan ba da tuni rikicin ya iso kasar Lebanon, da tuni an fara ganin motoci da bama-bamai suna tashia  acikin Lebanon kamar yadda suke tashia  biranan Iraki, ya ce a halin yanzu Syria tana gab da samun nasara a kan kyngiyoyin ‘yan ta’adda da aka kwaso daga kashen duniya suna kashe al’ummar kasar da sunan jihadi, kamar yadda a zahiri kasashen da suke kashe biliyoyin daloli wajen kwaso su da ba su makamai sun fara nuna gajiyawa dangane da hakan.
1410885

Abubuwan Da Ya Shafa: nasrallah
captcha