Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a wani taro da aka gudanar a karamin ofishin jakadancin Iran da ke kasar Tanzani, jakadan Palastinu a kasar ya bayyana cewa saka ranar Qods ta duniya a matsayin daya daga cikin muhimman ayyuka da marigayi Imam Khomeni (QS) ya gudanar a cikin rayuwarsa wanda al’mmar musulmi ba za su taba mantawa da wannan babban kokari da wannan mutum mai girma ya yi ba. A wani labarin kuma wasu yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun yi cincirindo a yau a gaban babbar kofar masallacin Qods, domin tunawa da cika shekaru 46 da yahudawan sahyuniya suka mamaye birnin Qods da kuma kwace iko das hi daga hannun Palastinawa. Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa yahudawan masu tsattsauran ra'ayi sun afka a cikin harabar masallacin ne a yau Talata, kuma suna ta yi zantuttuka na batunci ga musulmi da addinin muslunci, daga cikinsu kuwa hard a wasu fitattun 'yan siyasa daga jam'iyyar Likud, inda suke cewa Qods ta yahudawa ce ba ta musulmi ko larabawa ba. Kungiyoyin palastinawa 'yan gwagwarmaya bayan yin Allawadai da kakkausar murya kan wannan mummunan aiki, sun bayyana cewa wannan aiki ne na cin zarafin dukkanin al'ummar musulmin duniya, kuma hakan ya tabbatar wa duniya cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ba a shirye take ta amince da hakkokin al'ummar palastinu ba. 1429396