Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-yaum Sabi cewa, ana shirin girmama makaranta da mahardata kur'ani main a kasar a ranar idin karamar salla mai zuwa da nufin kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba da bayar da kwazo a karatunsu da kuma harda. A wani labarin na daban an kashe wani jami’in sojan kasar Masar guda a yankin Sina. Tashar telbijin din Presstv ta nakalto majiyar tsaron kasar Masar na fadin cewa an kashe sojan ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida daga wurin aiki a garin al-Arish da ke gundumar Sina. Majiyar tsaron masar ta ce maharan sun gudu bayan da su ka kashe sojan, sai dai an baza koma domin kamo su. A ranar talatar da ta gabata mai dai majiyar sojan Masar ta sanar da samun nasarar rusa wasu sansanoni ‘yan ta’adda a cikin yankin Sina tare kuma da kashe bakwai daga cikinsu. 1431907