
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Sirajul Haq shugaban kungiyar masu kishin islama a kasar Pakistan ta yi kakkausar suka da yin Allawadai kan yadda kasashen duniya suka yi shiru dangane da zubar da jinin palastinawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan take hakkokin bil-Adama da aiwatar da laifukan yaki a yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan yankin Zirin Gaza.
Kwamitin binciken zai gudanar da ayyukansa ne domin bankado hakika dangane da zargin cewa bangarorin da suke yaki da juna a Palasdinu wato gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Palasdinawa sun take hakkokin bil-Adama tare da tafka laifukan yaki, kuma kwamitin binciken zai fara yin nazari ne tun daga batun harin wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan yankin Zirin Gaza a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2013.
Kwamitin binciken na kasa da kasa zai gudanar da ayyukansa ne karkashin jagorancin William Schabas farfesa kan ilimin dokokin kasa da kasa dan kasar Canada gami da Dudu Deen kwararren masani kan harkokin doka dan kasar Senegal da kuma Amal Ilamuddeen wata shahararriyar lauya ‘yan asalin kasar Lebanon da take zaune a kasar Birtaniya.
Ana sa-ran kwamitin binciken na kasa da kasa zai kammala gudanar da ayyukansa tare da mika rahoton sakamakon binciken a cikin watan Maris na shekara ta 2015 mai zuwa.
1438015