
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga Kamfanin dillancin labaran Afrika daga birnin Bangi ya bayyana cewa Shugaba Catrina Samba ta zabi Mohammad Kamoon ne a jiya Lahadi, sannan kafin zabensa yana rike da kujerar mai bata shawara ne ta musamman a kan harkokin siyasar kasar.
A lokacin shugabancin Fransua Bozize Mohammad Kamoon ne babban ma’ajin kudaden kasar, wannan nadin ya zo nen makonni biyu kacal da bangarorin kiristoci da musulmin kasar Africa ta tsakiya suka cimma yerjejeniyar tsagaita bude wuta.
Babbar matsalar kasar Africa ta tsakiya a halin yanzu shi ne samun hanyoyin da za’a shawo kan kungiyoyin da suke dauke da makamai su amince da tattaunawa da kuma shiga gwamnatin kasar.
Kasar Africa ta tsakiya dai ta fada yakin basasa fiye da shekara guda. Yakin dai ya yi sanadiyyar rashin rayuka da dama da kuma tilastawa miliyoyi zama yan gudun hijira ko a cikin kasar ko a kasaashen waje.
1438435