IQNA

Na Rubuta Kur'anai Kwafi 6 Na Karshe Ina Da Shekaru 95

17:59 - August 20, 2014
Lambar Labari: 1441528
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin manyan malamai marubuta kur'ani mai tsarki a kasar Masar Sheikh Mahmud Ibrahim salamah ya rubuta kur'ani na karshe yana dan shekaru 95 da haihuwa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da jaridar Al-ahram ta kasar Masar ta yi da Sheikh Mahmud Ibrahim salamah daya daga cikin manyan malamai marubuta kur'ani mai tsarki a kasar Masar ya bayyana cewa, ya rubuta kur'anai da dama  arayuwarsa har a lokacin tsufa.

A bangare guda kuma a wani labarin na daban rundunar sojin Masar ta sanar da kashe ‘yan ta’adda 60 tare da kame wasu 102 na daban a samamen da sojojin kasar suka gudanar a yankin Tsibirin Sina.
Majiyar rundunar sojin Masar ta bayyana cewa; A samamen da sojojin gwamnatin kasar suka gudanar na tsawon kwanaki 12 a sassa daban daban da suke yankin Tsibirin Sina da nufin murkushe ‘yan ta’addan da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan jami’an tsaron Masar, sojojin gwamnatin Masar sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda akalla 60 tare da kame wasu 102 na daban.
Tun bayan kifar da gwamnatin Mohammad Morsi na kungiyar ‘yan uwa musulmi a Masar a ranar 3 ga watan Yulin shekara ta 2013, kungiyoyin ‘yan ta’adda suka nemi mayar da yankin Tsibirin Sina na kasar tungar ta’addanci ta hanyar kadamar da hare-haren wuce gona da iri kan jami’an tsaron Masar.
1440876

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha