IQNA

An Bayyana Salon Mulkin Isra'ila Da Na Wariya Irin Na Afirka Ta Kudu

23:23 - August 28, 2014
Lambar Labari: 1444084
Bangaren kasa da kasa, an bayyana salon mulkin da haramatcciyar kasar Isra'ila take yi kan al'ummar palastinu da cewa ya yi kama da irin salon mulkin da aka yi a kasar Afirka ta kudu na nuna wariya ga bakaken fata a lokutan baya.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, Ert Alyor wani fitaccen marubucin fim kuma mai wasan fina-finai a Amurka, ya bayyana salon mulkin da haramatcciyar kasar Isra'ila take yi kan al'ummar palastinu da cewa ya yi kama da irin salon mulkin wariya na Afirka ta kudu.

Shi ma tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu thabo mbeki ya jaddada kiransa ga al'ummomin kasar das u kaurace wa sayen kayayyakin da kamfanonin Isra'ila suke samarwa, mbeki ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wata lacca da daliban jami'ar birnin Pretoria suka shirya a daren jiya domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu.

Mbeki ya ce yana kira ga jam'iyyun siyasa da malaman addini da kuma kungiyoyin farar hula na kasar Afirka ta kudu, da su samar da wani shiri na kamfe a tsakanin al'ummar kasar na neman kaurace duk wasu kaya na Isra'ila, saboda kisan kiyashin da take yi wa fararen hula a Gaza.
A ranar Asabar da ta gabata ce kimanin mutane 50,000 suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Capetown domin yin Allawadai da Isra'ila da kuma kisan kiyashin da take yi kan mata da kananan yara a yankin Zirin Gaza.
1443062

Abubuwan Da Ya Shafa: HKI
captcha