Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran AFP cewa, mujallar kasar Faransa mallakin jam'iyyar socialist ta rubuta kalaman batunci ga wani ministan kasar wanda asalinsa musulmi saboda tsanin kyma ga mabiya addinin muslunci a kasar.
A wani rahoton mutane biyu musulmi suke rasa rayukansu a wani artabu da aka yi tsakanin sojojin kasar Faransa da kuma wasu daruruwan musulmi masu zanga-zanga a birnin bangui na Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
Rahotanni sun ce sojojin Faransa sun yi harbe-harbe da bindiga domin tarwatsa daruruwan musulmin, wadanda suke nuna damuwa dangane da irin halin da aka jefa su a kasarsu, inda suka yi ba-ta-kashi tsakaninsu da sojojin na Faransa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2 daga cikin musulmin wasu fiye da 20 kuma suka samu raunuka.
Shedun gani da ido sun ce masu zanga-zangar sun dauki gawawwakin mutanen biyu zuwa babban ofishin majalisar dinkin duniya da ke birnin Bangui domin tabbatar wa duniya irin cin fuskar da sojojin kasar ta Faransa ke yi musu a cikin kasarsu.