IQNA

Bayyana Hakikanin Musulunci Shi Ne Hanyar Yaki Da Akidar Takfiriyya

18:50 - September 10, 2014
Lambar Labari: 1448979
Bangaren kasa da kasa, babbar hanyar yaki da mummunar akidar nan ta takfiriyya it ace bayyana wa musulmi hakikanin abin da ake nufi da addinin muslunci da kuma koyarwarsa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron manyan malaman addinin muslunci na kasashen musulmi kan taimakon palastinu da aka gudanar a birnin Tehran sheikh Naim Kasim mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa hanyar yaki da mummunar akidar nan ta takfiriyya it ace bayyana wa musulmi hakikanin abin da ake nufi da addinin muslunci da kuma koyarwarsa mai tsarki.
Sheikh Na’im Kasim y ace an bayyana r wannan mummunar akida ta kafirta musulmi da kuma kashe su kamar dabbobi babu ji ba gani a wannan lokaci, wanda musulmi suke bukatar hadin kai da kara fahimtar juna domin fuskantar kalu bale da ke a gabansu, kuma hakan yana da alaka ne da shirin da makiya musulunci suka yi ne na rarraba kan musulmi, da kuma kokarin bata sunan wannan addini.
A jiya ne dai aka bude bababn taron malamai na addinin musulunci daga kasashen duniya daban-daban domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen taimakon al’ummar palastinu marassa kariya, wanda kuma hakan ya zo ne a daidai lokacin da ake cikin yanayi tsagaita bude wuta, kuma a cikin wannan lokacin an samu shigar da wasu kayan agaji ga al’ummar Gaza daga kasar Iran tare da taimakon Masar.
1448359

Abubuwan Da Ya Shafa: Kasim
captcha