IQNA

Ana Fito Na Fito Tsakanin Gwagwarmaya Karkashin Iran da kuma Amurka Da Takfiriyya

17:58 - September 14, 2014
Lambar Labari: 1450012
Bangaren kasa da kasa, ana yin fito na fito a yankin gabas ta tsakanin gwagwarmaya karkashin jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma Amurka da ‘yan korenta ‘yan takfiriyya da ke nufin rusa yankin baki daya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya sheda cewa, a zantawar da ya yi da Sheikh Na’im Kasim mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbollah a Lebanon ya bayyana cewa, a halin yanzu ana dauki ba dadi ne a yankin gabas ta tsakanin gwagwarmaya karkashin jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma Amurka da ‘yan korenta kuma karnukanta na farauta yan takfiriyya da ke nufin rusa yankin da al’ummominsa da kuma bakanta sunan addinin muslunci a duniya, amma saboda wasa da hankulan al’ummomin shi ne yanzu Amurka ta fara kada kugen yaki kan ‘yan ta’addan Takfiriyya saboda kashe Amurkawa biyu da suka.
Wannan kidan kugen yaki da Amurka ke yi kan 'yan ta'addan  ya zo ne bayan kwashe sama da watanni uku da kungiyar ta yi tana rike da yankuna da dama a arewacin kasar Iraki, inda ta kashe dubban mutane fararen hula tare da mayar da wasu miliyoyi 'yan gudun hijira, amma Amurka ba ta taba nuna alamar damuwa kan hakan ba.

Kafin wannan lokacin dai kungiyar ta IS ta kwashe sama da shekaru biyu tana gudanar da irin wadannan ayyuka na ta'addanci kan fararen hula a Syria, inda ta kashe dubun-dubatar mutane mata da kananan yara da sunan jihadi a tafarkin sunnah, ba tare da Amurka ta yi koda Allawadai ne da hakan ba, a maimakon hakan ma Amurka tana kiran wadannan 'yan ta'adda na kungiyar Alkaida da suka fito daga kasashen duniya daban-daban da sunaye daban-daban a matsayin masu fafutuka ko 'yan adawa da ke gwagwarmayar kafa dimokradiyya a Syria.

Babu wani abu da yake boye dangane da yadda aka kafa kungiyar , da kuma irin gudummawar da ita kanta Amurka ta bayar wajen yin hakan domin haifar mummunan yanayi na rikicin mazhaba a Iraki tun bayan kifar da Saddam Hussain, inda tun daga lokacin ISIS suka fara kashe mabiya mazhabar shi'a da sunan yaki da Amurkawa 'yan mamaya, wanda kuma bayan ficewar Amurkawa daga Iraki hare-haren nasu sun kara munana ne, kafin daga bisani kuma Amurka da sauran kawayenta na turai da 'yan kanzaginta daga cikin Larabawa su bude shafin rikicin kasar Syria bayan kifar da gwamnatin Gaddafi a Libya.

A jiya Laraba shugaban Amurka Barack Obama ya sanar da shirinsa na yaki da 'yan ta'addan, ta hanyar kai hare-hare kan sansanoninsu a cikin Iraki da Syria, kuma a kan haka ne ma a yau Alhamis wakilan kasashe arba’in da suke kawance da Amurka za su tattauna a birnin Jidda na kasar Saudiyya, amma daga cikin wadanda aka gayyata zuwa taron babu Rasha, Iran da kuma Syria.

Babban abin da ya sanya wasu masu bin diddin lamarin diga ayar tambaya kan wannan shiri na Amurka shi ne, yadda ita kanta Amurka da kawayenta na turai musamman Birtaniya da Faransa, gami da kasashen Saudiyyah, Qatar, Turkiya da kuma Joradan suka zama a sahun gaba wajen shirya taron daukar matakin yaki da kungiyar, alhali wadannan kasashe su ne suke da hannu wajen kafa kungiyar tare da daukar nauyin dukkanin ayyukanta, tare bata muggan makamai da makudan kudade da horarar da dubban mambobinta a cikin kasashen Jordan da haramtacciyar kasar Isra'ila.

1449474

Abubuwan Da Ya Shafa: Kasim
captcha