IQNA

Gidan Radiyon Mauritaniya Zai Fara Shirin Koyar Da Kur'ani Da Hadisai

19:36 - September 17, 2014
Lambar Labari: 1451248
Bangaren kasa da kasa, gidan radiyon gwamnatin Mauritaniya zai fara gudanar da wani shiri na koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki da sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bababn kamfanin dillancin labaran kasar Mauriya cewa gidan radiyon gwamnatin kasar zai fara aiawatar  da wani shiri na koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki da sunnar manzon Allah wanda za a rika watsawa kai tsaye a gidan radiyon.

Bayanin ya c an gudanar da zaman taro wanda a nan ne aka sanar da wannan shiri, daga cikin wadanda suka halarci taron kuwa har da ministan kula da harkokin al'adu da kuma ministan na ilimi a kasar, gami da wasu daga cikin manyan jami'ai na bangaren sadarwa da kuma malaman addini da sauran bangarorin na yan jarida da kuma masana da marubuta.

An fara aiwatar da shirin farko a matsayin gwaji a gidan radiyon, inda aka fara da bayani kan hadisan manzon Allah da kuma matsayinsu wajen bayyana addini da koyarwarsa ga musulmi, abin da aka fara shi ne tabo wasu daga cikin abubuwan da suka shafi raywar marubucin littafin hadisi na mabiya tafarkin sunna wato Bukhari wanda aka fi sani da Imam bukhari, wadanda aka haife shi a cikin shekara ta 194 hijira Kamariyyah, kumaya rasua  cikin shekara ta 256.

Malamin ya tattara hadisai masu tarin yawa inda ya hada su a cikin littafinsa da aka fi sani sahih Bukhari, kuma shi wannan littafi yana daga cikin manyan littafan mabiya sunna a duniya.

1450533

Abubuwan Da Ya Shafa: mauritania
captcha