IQNA

Rikice-Rikice A Cikin Tarihi Da Kuma Komawa Zuwa Ga Kur'ani

23:01 - September 19, 2014
Lambar Labari: 1451458
Bangaren kasa da kasa, tsohon ministan harkokin wajen kasar Sudan ya gabatar da wani littafinsa da ya rubuta dangane da wasu daga cikin matsaloli da suka faru da kuma matsayin kur'ani mai tsarki a kansu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, Mustafa Usman Isma'il tsohon ministan harkokin wajen kasar Sudan kuma ministan mai kula da harkokin saka hannayen jari a halin yanzu ya gabatar da wani littafinsa da ya rubuta dangane da wasu daga cikin matsaloli rikice-rikice da suka faru da kuma matsayin kur'ani mai tsarki a kansu da yadda ya yi bayani dangane da su.

An gudanar da wani zama a babban dakin gudanar da taruka na jami'ar Ummu-Durma a kasar ta Sudan, inda a nan ne aka gabatar da jawabai dangane da wannan littafi da kuma bayyana mahanga ta ilimi a kansa, inda shi kansa ministan tare da wasu jami'an gwamnati da kuma manyan malaman jami'oi suka halarci taron tareda gabatar da jawabansu.

A lokacin da yake karin haske kan wasu bangarorin littafin, ministan ya bayyana cewa a kowane lokaci addinin muslunci yana daukar matsayi na kare kai ne a cikin batutuwa da suka shafi yaki da ya wakana tsakanin musulmi da wasu al'ummomi, wanda kuma wannan batu na daga cikin abin kan sanya wasu kasa gane matsayar musulunci dangane da batun jihadi.

Ya ce kur'ani mai tsarki yana umarta musulmi ne da su jihadi wajen kansu da addininsu daga masu cutar da su ko kuma yi musu barazana, domin kuwa musulmi sun zauna tare da wadada ba musulmi a Madina da sauran wurare bayan da suka dauki alkalin kiyaye hakkokin musulmi ba tare da cutar da su, kamar dai yadda tarihin muslunci ya tabbatar da hakan.

1451211

Abubuwan Da Ya Shafa: sudan
captcha