IQNA

Tsatsauran Matakin Azhar Kan Tafiyata Zuwa Iran Yana Ban Mamaki

23:26 - September 21, 2014
Lambar Labari: 1452346
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Ahmad Karimah daya daga cikin malaman Azhar ya bayyana cewa irin matakin da jami'ar Azhar ta dauka dangane da tafiyarsa zuwa Iran yana da matukar ban mamaki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almisriyun cewa, Sheikh Ahmad Karimah ya bayyana cewa tafiyarsa zuwa Iran ta zama sanadiyyar zama wani tushen rikici maras dalili a cikin jami'ar Azahar, wanda kuma babban dalilin tafiyar ba komai ba ne illa ziyara da kuma ganewa ido irin abubuwa da mazhabar Ahlul bait ta dogara da su wajen kafa hujjoji da kuma ji daga bakin ma'abota mazhabar.

Malamain ya fuskanci matsaloli tare da malaman jami'ar Azahar a cikin makon da ya yi wata tafiya zuwa kasar Iran, inda ya gana da manyan malamai na mazhabar Ahlul bait, lamarin da ya sanya jami'ar daukar mataki na gudanar da bincike a kansa, daga bisani kuma aka sanar da dakatar da koyarwar a bangaren shari'a kamar yadda ya saba, bisa hujjar cewa ya gana da malaman mazhabar Ahlul bait a Iran.
Ya ce abin mamaki shi ne yadda jami'ar ta dauki dukaknin mamzhabobi tana koyar da su har da mazhabar batattu, wadanda kowa ya yi imanin cewa akidunsu sun hannun riga da koyarwar addinin muslunci, amma duk da haka cibiyar Azahar ta mayar da wannan mazhaba daga cikin mazhabobin da ake koyarwa,a  cikin masar har da wajen kasar a rassan jami'ar.
Ya kara da cewa zai ci gaba da gudanar da bicike domin zama mai fadada saninsa kan  dukkanin ilmomi na mazhabobin musulunci, maimakon zama a cikin duhu kana bin da wasu suka rike shi bisa dogaro da hujjojinsu.
1452109

Abubuwan Da Ya Shafa: Karima
captcha