IQNA

Taron Bayar Da Horo Kan Harhada Fina-Finan Tarihi A Sudan

16:56 - September 23, 2014
Lambar Labari: 1453292
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro wanda a cikinsa ake horar da wasu mahalrta kan yadda ake hada tarihin muslunci a cikin fim wanda zai kunshi wurare da kuma mutane da suka taka rawa.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi da ake bugawa  akasar Masar cewa, a jiya a birnin Khartum an fara gudanar da wani zaman taro wanda a cikinsa ake horar da wasu mahalrta kan yadda ake hada tarihin muslunci a cikin fim wanda zai kunshi wurare da kuma mutane da suka taka rawa a fagage na tarihi.

Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyar bunkasa harkokin aladu da kuma ilmi na kungiyar kasashen msuulmi ISECO c eta dauki nauyin shirya wannan taro na horar da maana tarihi wadanda suka ke karatu a jami'ar birnin Khartum, inda suka fara samun horo kan yadda ake harhada fina-finan tarihi ta hanyar zuwa wurare da kuma ganawa dam asana tarihi an kasar da kuma malaman jami'a.

Sudan tana daya daga cikin kasashen nahiyar Afirka kuma daya daga cikin manyan kasashen musulmi da suke bayar da gagaruwar gudunamwa wajen yada ilimin addinin muslunci kuma tarihin addini da yaduwarsa a duniya da kuma nahiyar Afirka.

Wanann horo yana da matukar muhimamnci ta fuskoki da dama da hakan ya hada bangaren yada a'adun muslunci ga sauran al'ummomin duniya musamamn ma wadanda ba musulmi ba.

1452277

Abubuwan Da Ya Shafa: khartum
captcha