Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, a zantawar da ya yi tare da shugaban bangaren Afirka da kasashen larawaba na Majma Ahlul-bait (AS) Hassan Khakrand ya bayyana cewa ana samun ci gaba a Najeriya ta fuskar yaduwar mazhabar Ahlul bait duk da kalu bale da ake fuskanta daga wahabiyawa masu kiyayyah da mazhabar Ahll bait (AS)
A makon karshe na watan azumi ne aka gudanar da jerin gwanon ranar Quds a birnin Zariya da ke cikin jahar Kaduna, wanda ‘yan uwa muuslmi mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky suka jagoranci gudanarwa, domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu, kamar dai yadda aka saba gudanarwa tsawon shekaru a birnin na Zariya da ma wasu birane na tarayyar Najeriya.
Sai dai a wannan karon jami’an sojin Najeriya sun afka kan wadanda suka gudanar da wannan jerin gwano, inda suka kashe mutane fiye da 30, daga cikinsu kuwa har da ‘ya’yan Sheikh Zakzaky guda uku, kashe gari kuma sojojin sun sake kaddamar da wani harin a kan cibiyar Bakiyyatullah, wurin da Sheikh Ibrahim Zakzaky ke bayar da karatu da kuma gudanar da taruka na addini, inda rahotanni suka ce sojojin sun kashe akalla mutane uku a wurin tare da jikkata wasu.
Jim kadan bayan hakan Sheikh Zakzaky ya zanta da manema labarai, inda ya fayyace hakikanin abin da ya faru a jerin gwanon ranar Quds a Zariya, ya tabbatar da cewa sojojin da aka turo sun bude wuta ne kan masu jerin gwano na lumana, wadanda ba su dauke da komai sai kwalaye da kyallaye da aka yi rubuce-rubuce kansu na nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu, wanda kuma an saba gudanar da hakan tsawon shekaru ba tare da wata hatsaniya ba. Sheikh Zakzaky ya yi kira ga dukkanin 'yan uwa musulmi da su kwantar da hankalinsu dangane da abin da yake faruwa a Zariya, wanda ya kamanta shi da abin da yake faruwa kan musulmi a Gaza.
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa Kasar Amurka tana da hannu a hare haren ta'addancin da ake kai wa a Nigeriya kungiyar Boko Haram sananniyar kungiya ce, amma Amurka tana zargin wasu kungiyoyi a Nigeriya da hannu a kai hare hare a kasar saboda ta raunana al'ummar musulmi tare da rarraba kansu.
Har ila yau Sheikh Zakzaky ya bayyana cewar mutanen da suke bayyana kansu a matsayin masu magana da yawun kungiyar Boko Haram a Nigeriya wakilan kasashen waje da ba su da wata alaka da koyarwan Musulunci.