IQNA

Sayyid Nasrullah ya Gabatar Da Jawabi Kan Abubuwan da ke Faruwa A Gabas Ta Tsakiya

16:45 - September 24, 2014
Lambar Labari: 1453787
Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sayyeed Hassan Nasarallah ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurca bata cancanta jagorantar kawance na masu yaki da ayyukan ta'addanci a duniya, ba.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Aslab News cewa, Shugaban ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurca ce fi ko wace kasa aduniya goyon bayan ayyukan ta'addanci, kuma ta goyi bayan HKI a hare haren ta'addancin na kwani 51 da ta kaiwa yankin Gaza na Palasdini a cikin yan kwanakin da suka gabata. Banda haka tana ci gaba da goyon bayan yan ta'adda da dama a yankin.

Sayyeed Nasarallah ya ce , banda haka gwamnatin shugaban Baraka Obama ta fito fili ta bayyana cewa tana yakar kungiyar Da'eesh ne don masalahar ta a yankin, don haka mu kuwa bama tare da duk wata maslahar kasar Amurca a yankin, inji shi.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya bayyana haka ne a wani jawabin da ya yi a jiya da dare a wasu tashoshin television na gabas ta tsakiya wadanda suka hada da television na Almanar da Almayadeen na kasar lebenon.

Shugaban kungiyar ya kara da cewa kungiyar Hizbullah tana yakar kungiyoyin yan ta'adda wanda ya hada da kungiyar Daeesh kuma zata ci gaba da hakan, amma kungiyarsa bata goyon bayan gwamnatin kasar Lebanon ta shiga cikin kawancen yaki da ta'addanci wanda kasar Amurca take jagoranta a kasashen Syria da Iraqi.

1453008

Abubuwan Da Ya Shafa: nasrallah
captcha