IQNA

22:39 - October 06, 2014
Lambar Labari: 1457587
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Shauat Aljundi shugaban babbar cibiyar bincike kan harkokin muslunci a Masar tare da masana da dama sun nuna bacin ransu matuka dangane da abin da mujallar kasar faransa ken a cin zarafin manzon Allah (SAW) a cikin lokutana nan.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Misral yaum cewa, shugaban babbar cibiyar bincike kan harkokin muslunci a Masar  Muhammad Shauat Aljundi tare da masana da dama sun nuna bacin ransu matuka dangane da abin da mujallar kasar faransa ken a cin zarafin manzon Allah (SAW) da nufin tsokanar muslmi.

A jamhuriyar muslunci ma dai dubban mutane ne suka gudanar da wani taron gangami a gaban ginin ofishin jakadancin kasar Fransa da ke fadar mulkin kasar, a wannan karo domin nuna fushinsu dangane da zanen batanci mai siffanta manzo rahma mai tsira da amincin Allah da kuma iyalan gidansa tsarkaka da wata jaridar kasar Faransa mai suna Charlie Hebdo ta wallafa a fitowarta ta jiya.

A nashi bangare kuwa kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, wanda yake mayar da martani dangane da wannan zane na batanci da jaridar kasar Faransa ta buga, ya bayyana cewa shirun da kasashen Yamma ke yi a game da shirya fina-finai ko kuma yin zane-zane irin wadannan, abubuwa domin cin zarafin addinin musulunci, wata alama ce da ke kara tabbatar wa duniya matsayin kiyayyar da ake nunawa musulmi a wadannan kasashe tare da yardar gwamnati.

Ko baya ga wannan gangami da aka gudanar a harabar ofishin jakadancin Faransa da ke nan, wasu dubban mutanen sun gudanar da wata zanga-zanga a dandalin Palasdinu da ke tsakiyar birnin bisa gayyatar kungiyar masu rajin kare Alkur'ani mai girma, inda suka yi tir da kuma Allah wadai da abubuwa na rashin hankali da ake aikatawa a Amurka da kuma wasu kasashen Yammacin Turai domin kawai cin zarafin addinin Allah.

1457387

Abubuwan Da Ya Shafa: Misra
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: