IQNA

20:27 - October 10, 2014
Lambar Labari: 1458731
Bangaren kasa da kasa, za a bude reshen bankin musulunci a kasar Burkina Faso wanda zai rika gudanar da harkokinsa daidai kaidoji na mu'amalar da addinin muslunci ya amince da ita.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar CNN cewa, nan bad a jimawa ba za a bude reshen bankin musulunci a kasar Burkina Faso da ke yammacin Afirka wanda zai rika gudanar da harkokinsa daidai kaidoji na mu'amalar da addinin muslunci kamar yadda ake gudanar da hakan a wasu kasashe.

Rahoton ya ce daya daga cikin manyan bankuna na kasar ne zai dauki nauyin bude reshen bankin muslunci bayan gudanar da bincike kan tasirin da zai yi a kasar wadda ke da yawan mabiya addinin muslunci, bayan samun lasisin hakan daga babban bankin kasar, inda yanzu haka da dama daga cikin 'yan kasuwa na kasar da kuma masu mu'amala da kudade suka nuna sha'awarsu ta yin mu'amala da wannan banki, da hakan ya hada da musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba.

Kasar Burkina Faso dai tana mutane da suka kai kimanin miliyan 17 kuma fiye da kashi 60 ckin dari daga cikinsu mabiya addinin musulunci ne, yayin da sauran mutanen kuma sun hada da mabiya addinai daban-daban daga ciki hard a mabiya addinin kirista, gami da kuma masu bin addinan gargajiya na Afirka.

1458525

Abubuwan Da Ya Shafa: Burkina
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: