IQNA

ISESCO Ta Yaba Da Matsayin Da Gwamnan Lille Ya Dauka Kan Isra’ila

15:00 - October 11, 2014
Lambar Labari: 1459159
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da a’adu ta kasashen musulmi ta yaba da irin matakan da mahukuntan birnin Lille na kasar Faransa suka dauka kan haramtacciyar kasar Isra’ila.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, Abdulaziz bin Usman Al-tuwaijari babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da a’adu ta kasashen musulmi ya yaba da irin matakan da mahukuntan birnin Lille na kasar Faransa suka dauka kan haramtacciyar kasar Isra’ila na nuna mata rashin amincewa da zaluncinta kan al’ummar palastinu.

Bayanin ya ci gaba da mahukuntan na birnin Lille musammn ma gwamnan jahar wanda mai bin akidar kwaminisanci ne ya nuna wa haramatcciyar kasar Isra’ila cewa bad k abin da take yi ne ba zai zama karbabbe ga al’ummomin duniya, kuma ta’addancinta na baya-bayan nan kan mata da kanan yara a Gaza ya tabbtar wa duuniya kowace Isra’ila.

A nasa bangaren babban sakataren kungiyar ta ISESCO ya yi kira ga sauran mahukunta  abiranan kasar Faransa da su dauki irin wannan mataki kan Isara’ila, domin ta san cewa duniya ta sane kana bin da take aikatawa na barna da cin zalun kan al’ummar Gaza marassa kariya, kuma duniya ba ta tare da ita a cikin wannan aiki na zalunci da danniya da babakere.

1459013

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha