IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Tozarta Masallacin Qods

21:51 - October 15, 2014
Lambar Labari: 1460701
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kaakusar suka tare da yin Allawadai da matakan da haramatcciyar kasar Isra’ila take dauka na cin zarafin musulmi da kuma tozarta masallacin Qods mai alfarma


Kamfanin dilancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran Qods Press cewa kungiyar kasashen musulmi ta yi kaakusar suka tare da yin Allawadai da haramatcciyar kasar Isra’ila kan cin zarafin musulmi da kuma tozarta masallacin Qods mai alfarma da take  ayi a cikin kwanakin nan.

A nasu bangaren wasu yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun yi cincirindo a yau a gaban babbar kofar masallacin Qods, domin tunawa da cika shekaru 46 da yahudawan sahyuniya suka mamaye birnin Qods da kuma kwace iko das hi daga hannun Palastinawa.  

Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa yahudawan masu tsattsauran ra'ayi sun afka a cikin harabar masallacin ne a yau Talata, kuma suna ta yi zantuttuka na batunci ga musulmi da addinin muslunci, daga cikinsu kuwa hard a wasu fitattun 'yan siyasa daga jam'iyyar Likud, inda suke cewa Qods ta yahudawa ce ba ta musulmi ko larabawa ba.  

Kungiyoyin palastinawa 'yan gwagwarmaya bayan yin Allawadai da kakkausar murya kan wannan mummunan aiki, sun bayyana cewa wannan aiki ne na cin zarafin dukkanin al'ummar musulmin duniya, kuma hakan ya tabbatar wa duniya cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ba a shirye take ta amince da hakkokin al'ummar palastinu ba.

1460500

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha