Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a yau tattauna batun shishigin haramatacciyar kasar Isra'ila da kuma wuce gonad a irin da take yi ta hanayar saba dokokin kasa da kasa a cikin yankunan palastinawa a kwamitin tsaron.
Jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila sun jikkata Palastinawa fiye da 40 a yau a birnin Qods, yayin da kuma suka kame wasu kimanin 13 suka tafi da su zuwa wani da ba a sani ba.
Mai aikowa tashar talabijin ta Al-alam rahotanni daga birnin Qods ya habarta cewa, jami'an tsaron yahudawan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa daruruwan matasa da suka taru a cikin harabar masallacin Qods mai alfarma, inda suka yi ta antaya barkonon tsohuwa acikin masallacin, tare da yin harbi da bindiga, inda suka jikkata mutane fiye da 40 kuma suka kame wasu 13.
A cikin makon da ya gabata ne 'yan sandan yahudawan Isra'ila suka rufe masallacin Qods baki daya, tare da hana musulmi yin salla a cikinsa, kasashen musulmi da na larabawa dai suna ci gaba da yin gum da bakunansu, dangane da wannan ta'asa da yahudawan suke aikatawa kan al'ummar musulmin palastinu da kuma masallacin Qods mai alfarma.