Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa George Jarqan marubuci tarihi kirista wanda ya yi rubutu mai yawa kan Imam Ali (AS) ya bar gidan duniya yana da shekaru 83 da haihiwa bayan fama da rashin lafiya, wadda daga karshe ta yi sanadiyyar rasuwarsa.
Wannan marubuci dai ya rubuta littafai da dama da suka shafi rayuwar Imam Ali (AS) da ke nuna matsayin Imam da cewa shi mutum na musamman wanda ya zama a bin koyi ga dukkanin mutanen duniya a dukkanin fuskoki na rayuwa, da suka hada da adalcinsa, tausayi siyasarsa zamantakewarsa da ilminsa a kan lamurra da kuma yadda yake tafiyar da komai a kan ilmi da hikima.
Dag acikin littafan da ya rubutu akwai littafin (Ali Sautin Adalcin ‘yan Adamtaka) (Ali Da Hakkin dan Adam) (ali Da Juyin Faransa) (Ali da Surat) (Ali da akidar ‘yan kasancin larabci) da dai sauran littafai da dama da yaruta kansa.
George Sam’an an haife shi ne a shekara ta 1931 a garin Marja’iyyun da ke kudancin kasar Lebanon.
1470548