IQNA

Ya Raya Kan Tarayyar Turai EU Ta Amince Da Kasar Palastinu A Hukumance

18:51 - November 06, 2014
Lambar Labari: 1470582
Bangaren kasa da kasa, tsohon ministan harkokin wajen kasar faransa Allen Joe ya bayyana cewa dole ne a yi adalcia cikin harkokin da suke gudana a kan al’ummar palastinu kuma baban abin yi shi ne a amince da kasarsu a hukumance.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na europel cewa, a wata zantawa ta goidan talabijin a jiya tsohon ministan harkokin wajen kasar faransa Allen Joe ya bayyana cewa bisa ga abubuwan da suke gudana a kan al’ummar palastinu babban abin yi ba a kan kasar Faransa ba kawaihar ma a kan kungiyar tarayyar turai shi ne a amince da kasarsu a hukumance maimakon daukar palastinu wani yankin Isra’ila kawai.
Ya ci gaba da cewa irin matakin da hukumar UNESCO ta dauka na amincewa da palastinu a matsayin kasa a hukumance babban abin yabo ne, kuma hakan yana kara karfafa gwiwa a kan cewa ya zama a wajibi a kan dukkanin kasashen turai da su dauki irin wannan mataki, kuma yin hakan zai taimaka wajen kawo zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Allen Joe ya kasance ministan harkokin wajen Faransa a cikin shekarun 1993-1995-2011-2012, kuma bababn mamba ne na jami’iyyar UMP, wanda ake sa ran zai tsaya takarar shugabancin Faransa a zaben shekara ta 2017.

1470275

Abubuwan Da Ya Shafa: France
captcha