Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Al-badil cewa, a jiya Muhammad Mukhtar Juma'a ministan ma'aikatar da ke kula da ayyukan addinin mulunci a Masar ya bayyana cewa dole ne a dauki matakan takawa yahudawa birki kan ta'addancin da suke tafkawa kan masallacin Aqsa.
A nata bangare guda kuma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta bayyana abin da ke faruwan a halin yanzu a birnin Quds da cewa, ya kara bayyana hakikanin siffar ta'addanci ta yahudawan Isr'aila da kuma kiyayyarsu ga musulmi.
Malamar ta kara da cewa kisan palastinawa da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da yahudawan Isra'ila suke yi musamamn a birnin Qods mai alfarma, ba abu ne da za a amince da shiba, a kan hakan ta ce ya zama wajibi a kan dukkanin kasashen musulmi da na larabawa su dauki mataki na bai daya domin fuskantar wannan lamari.