
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-nashra cewa, Shekh Na'im kasim mataimakin jagoran kungiyar Hizbullah ya bayyana dukkanin matsalolin da ake fuskanta a kasar Lebanon ta fuskar siyasa da tsaro da cewa yahudawan sahyuniya ne da hannu a cikinsu kai tsaye.
A kwanakin baya ne shi kansa jagoran kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa Amurka da Isra'ila sun yi wa kasashen yankin gabas ta tsakiya shiri na musamman da nufin daidaita su.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar yanzu bad a jimawa ba domin tunawa da cika shekaru 8 da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da hare-hare kan al'ummar Lebanon da sunan yunkurin murkushe Hizbullah, inda ya ce shirin Amura da Isra'ila na kaddamar da wannan yaki bai yi nasara ba, amma kuma har yanzu ba su gushe ba tare da wasu gwamnatocin larabawa na yankin suna kokarin aiwatar da wannan manufa ta rusa kasashen larabawa da kuma tarwatsa kasashen musulmi.
Malamin ya ce abin da yake faruwa a kan al'ummar Gaza da Iraki, da kuma Syria ci gaba na wannan shiri da Amurka da Isra'ila na tarwatsa kasashen musulmi, inda sukan shiga cikin shirin da kansu, kuma sukan sanya wasu gwamnatocin larabawa su aiwatar musu da shirin nasu.
1473437