IQNA

‘Yan Ta’adda Sun Karkata Ma’anar Ayoyin Kur’ani 50 Domin Su Halasta Ta’addanci

15:23 - November 18, 2014
Lambar Labari: 1474707
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa na kasar Sheikh Shauki Allam ya bayyana cewa masu aikata ta’addanci da sunan muslunci suna juya ma’anar aoyin kur’ani domin cimma burinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-Youm Al-Sabe cewa Sheikh Shauki Allam  babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana cewa masu aikata ta’addanci da sunan muslunci sun karkata ayoyin kur’ani guda 50 tare da  juya ma’anar wadannan aoyin kur’ani domin cimma manufarsu na ta’addanci.
Babban malamin addinin na kasar Masar Sheikh Shauqi Al-allam ya bayyana cewa kungiyar da ake kira Daular Musulunci a iraki da sham gungu ne na 'yan ta'adda tantagarya, a cikin wani bayani da ofishin da ke a cibiyar Darul Ifta a birnin Alkahira ya fitar a jiya Talata, Sheikh Al-allam ya ce 'yan ta'addan kungiyar ISIS bai halasta ba a shar'ance a danganta su da addinin musulunci, domin dukkanin abin da suke yin a ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen Syria da Iraki ya yi hannun riga da addinin muslunci da kuma koyarwar sunna irin ta manzon Allah.
Shehin malamin ya yi Allawadai da rusa kabrukan annabawa da salihan bayi gami da masallatai da majami'oi da 'yan kungiyar ta ISIS suke yi yanzu ahak a cikin kasashen Syria da Iraki, tare da muzantawa da kuma cin zarafin marassa rinjaye da suka mamaye yankunansu, musamman kiristoci da kuma Izidawa da kuma sauran bangarori na musulmi baki daya.
1474090

Abubuwan Da Ya Shafa: Allam
captcha