IQNA

Farmakin Daukar Fansa Kan Yahudawa A Birnin Quds Ya yi Daidai

21:27 - November 19, 2014
Lambar Labari: 1475305
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin palastinawa 'yan gwagwarmaya sun bayyana harin da wasu palastinawa suke kaiwa kan yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi a birnin Quds da cewa hakan ya yi daidai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Aljazeera cewa da dama daga cikin kungiyoyin palastinawa 'yan gwagwarmaya sun bayyana harin da wasu palastinawa suke kaiwa kan yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi a birnin Quds da cewa wannan abu ne mai kyau.

Majiyoyin asibitin Haramtacciyar kasar Isra'ila a birnin Quds sun ce daya daga cikin yahudawan da suka samu raunuka a lokacin harin daukar fansa da wasu Palastinawa suka kai jiya kan gungun wasu yahudawa a birnin na Quds ya rasa ransa.

Majiyar asibitin ta ce wannan shi ne ya cika adadin wadanda suka mutu zuwa yahudawa biyar sakamakon harin da wasu matasan palastinawa biyu wato Addiy da kuma Gassan Abu Jamal suka kai kan yahudawan sahyuniya a wani wurin bautarsu, inda suka halaka hudu daga cikinsu a nan take tare da jikatta wasu, da suka hada da wani daya daga cikin malaman yahudawan masu tsatsauran ra'ayi, 3 daga cikin wadanda suka mutu yahudawan Amurka ne, daga bisani 'yan Isra'ila sun harbe palastinawan biyu har lahira.

Wannan hari dai ya zo ne kwana daya bayan wani kisan gilla da wasu yahudawa suka yi wa wani bapalastine direban motar bas, inda suka shakare shi a cikin motarsa har said a ya motu. A nasa bangaren Firayi Ministan Haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Natanyahu ya bayar da umarni da a kame dangin Palastinawan da suka kaddamar da harin, tare da rushe gidajensu.

1475024

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha