IQNA

An Fara gudanar Da wani Zama Tsakanin Jami'ar Azhar Da Fadar Vatican

8:28 - February 25, 2009
Lambar Labari: 1748320
Bangaren kasa da kasa: A yau ne aka fara gudanar da wani zama tsakanin wasu wakilan jami'ar Al-azhar ta kasar maser, da kuma wakilan fadar Vatican a birnin Rom na kasar Italia.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na (MUHIT) cewa; an fara gudanar da taron ne tsakanin Azhar da Vatican ya a birnin Rom, da nufin kara karfa fahimtar juna tsakanin mabiya addinan kiristanci da musulunc. Wanda ya jagoranci tawagar Azhar zuwa birnin na Rom (Ali Abdulbaki) ya bayyana cewa; wajibi ga dukkanin bangarorin biyu wato musulmi da kirista da su karfafa fahimtar juna tsakaninsu, kasantuwar addinansu addinai ne da aka safkar daga sama, dole ne a samara da fahimtar juna mai dorewa tsakanin bangarorin biyu, wanda kuma hakan nauyi ne day a rataya kan jagororin addinan biyu.

368966





captcha