IQNA

Burin Kamawa da Tsare Yan Shi'a A Saudiya Haddasa Rarrabuwa a Tsakanin Musulmi

16:54 - March 01, 2009
Lambar Labari: 1750139
Bangaren siyasa: mamba a majalisar kwararru masu zaba da dubin aikin Jagora y ace kamawa da tsare yan shi'a buri ne na haddasa sabani tsakanin musulmi.
A rahoton da ta watsa cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ta nakalto ofishin Ayatullal Abas Ka'abi na cewa a wata tattaunawa day a yi da Shekh Jawad Alhadari malami a kasar Saudiya ya shaida masa cewa kamawa da tsare yan shi'a a Saudiya wani mataki ne da zai haddasa rikici da rarrabuwar kawunan musulmi a duniya kuma hakan zai iya shafar masu kai ziyara a wannan kasa .wannan mataki da wasu ke fakewa domin cimma wata manufa ta bobe da sakamakonta ba zai kasance alfanno a gare su ba ko shakka babu.

370371
captcha