IQNA

Kasashen Musulmi Dole Su Bullo Da Tsarin Bai Daya Na Tattalin Arziki

14:09 - March 04, 2009
Lambar Labari: 1751719
Bangaren kasa da kasa:Abdallah Ahmad Badawi firaministan kasar Indonoziya ya bukaci kasashen musulmi da su bullo da wani shiri na tattalin arziki na bai daya domin magance matsalar tattalin arziki da ke addabar duniya.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga kamfanin dillancin labaran AFP ta watsa rahoton cewa: Abdalla Ahmad Badawi a lokacin da yake bayani a zauren taron tattalin arzikin musulunci ya bayyana cewa; yana bukatar kasashe da suka halarci wannan taro da sauran wadanda bas u halarta bad a su zama abin koyi wajen magance matsalar tattalin arziki da ke addabar duniya a yau . ya kara da cewa: a yau tsarin tattalin arzikin da ke jan akalar duniya tsari ne na saye da sayarwa kuma na jari hujja ba tare da mutum ya mallaki abu sai ciniki da kudi cikin iska lamarin day a sha bamban a musulunci da kuma ya yi hani kan haka saboda haka kasashen musulmi ya kamata su bullo da wani tsari na bai daya na tattalin arziki.

372248

captcha