Cibiyar kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar shugaban kasar Iran ta watsa rahoton cewa: shugaban kasar Iran ahmadinajad yana bayyana cewa: ya kamata wasu kafafen watsa labarai na kasashen musulmi su fahimci makircin makiya addinin musulunci kuma makiyan musulmi da kasashensu da ke kokarin haddasa rikicin da sabani a tsakanin kasashen musulmi musamman a tsakanin Iran da wasu kasashen musulmi ta hanyar fuskantar juna. A yau lokaci ne da bai kamata ba al'ummar musulmi da kasashen musulmi za su hada kansu da fahimtar makircin makiyansu.
375305