IQNA

Mata Musulmi A Kasar Birtaniya Na Samun Horo Don Shiga Ayyukan Gwamnati

14:38 - March 12, 2009
Lambar Labari: 1755285
Bangaren kasa da kasa: Mata musulmi a kasar Birtaniya na samun horo da nufin shiga cikin harkokin siyasa da ma ayyukan gwamnati a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (APP) cewa; kungiyar mata musulmi na kasar Birtaniya ta fara aiwatar da wani shiri na bayar da horo ga mata musulmi da ke kasar, domin karfafa gwiwarsu wajen shiga cikin harkokin siyasar kasar, da ma ayyukan gwamnati, bisa la'akari da karancin shiga cikin harkokin da ke kai da komowa a kasar.
Rahoton ya ce ana bayar da horon ne a wasu cibiyoyin ilimi mallakin musulmi da kuma wasu dakunan gudanar da taruka da ke birane daban-daban na kasar.
Yanzu haka dai akwai mata musulmi sama da dubu 800 da suke rayuwa a kasar Birtaniya, wanda hakan ke nuni da muhimmancin da suke da shi a cikin al'ummar kasar.

376842

captcha