Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Barnama ta watsa labarain cewa; Ikmalul Dine Ihsan Uglu sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a lokacin bude taron kungiyar kasashen larabawa a Doha fadar mulkin kasar Katar ya jaddada cewa Haramtacciyar kasa Isra'ila na kokarin ruguza gidajen Palasdinawa da ke zaune a Kudus da kewaye ta hanyar ci gaba da gina matsugunnan Yahudawa yan share guri zauna . Saboda haka babu wani nauyi day a rataya a wuyanmu face taimakawa yan uwanmu musulmi da kawo karshen wannan cin zalin da gasa aya a hannu da Yahudawan sahayoniya ke yi wa yan uwanmu Palasdinawa. A bangare day a ya yi kira ga kasashen musulmi musamman larabawa da su gaggauta sake gina yankin Zirin Gaza.
381656