Bangaren siyasa: Wannan shi ne karo na talatin da biyu da kungiyoyin musulmi ke gudanar da taro kan tattalin arziki ,al'adu da zamantakewa karkashin inuwar kungiyar hadin kan kasashen musulmi OCI a kasar Saudiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kasar Koweiti Kuna ta watsa labarin cewa ; wannan taro na kwanaki uku ya hada wakilai daga kasashe 57 mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi kuma a bangare daya wakilin hukumar da ke kula da ilimi da al'adu na majalisar dinkin duniya ya halarci wannan taro mai matukar muhimmanci da abubuwan da za a tattauna a dakin taron a daidai wannan lokaci da matsalar tattalin arziki ke fuskantar manyan kasashe da neman mafita .Yayin da a dabra da haka kasashen musulmi da ke bin tsarin tattalin arziki irin na musulunci suke cikin daiodaito da nucuwa.
382510