IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Mazhabar Shi'a A Zamanin Da Da Na Yanzu

16:50 - April 12, 2009
Lambar Labari: 1763848
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani taro a jami'ar Galastari ta kasar Birtaniya kan mazhabar shi'a a zamunan dad a kuma zamanin yanzu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na jami'ar Galstrai cewa; Bangaren bincike kan ilimin sanin halayyar dan adam na jami'ar ne ya shirya gudanar da wannan zaman taro, inda masana da suka gudanar da bincike kan mazhabar shi'a da tarihinta za su gudanar da laccoci, tare da bayyana mahangarsu kan wannan mazhabar yadda ta kasance a lokutan baya, da kuma yadda take a halin yanzu a duniyar musulmi baki daya. Kamar yadda masana da za su gabatar da laccoci za su bayyana mahangar mazhabar shi'a kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar dan adam da tunaninsa da rayuwarsa ta zamntakewa gami da makomarsa. Daga cikin wadanda za su gudanar da laccocin kuwa hard a shugaban bangaren bincike kan ilimin sanin halayyar dan adam na jami'ar Chilly Chagvera, da kuma shugaban bangaren bincike kan ilimin addinin muslunci da harshen larabci na jami'ar Kent Great, gami da wasu malaman jami'a daga Oxford da wasu jami'oin Birtaniya.

386114

captcha