IQNA

A Wannan Shekara Za a Samu Karin Bankoki Masu Tsarin Musulunci

12:36 - April 14, 2009
Lambar Labari: 1764782
Bangaren zamantakewa; Mataimakin shugaban da ke kula da bada ilimi a hukumar yada al'adun musulunci ya bada labarin karuwar bankoki masu bin tsarin musulunci a wannan shekara.
Bayan ta nakalto daga hukumar da ke kula da yada addinin musulunci a Iran ,cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Hujjatul Islam Said Jawad Musawi Hawayi mataimakin shugaban da ke kula yada ilimi a wannan hukuma da ke kula da yada addinin musulunci ya bayyana cewa babban abin da hukumar za ta fi maida hankali kansa a wannan shekara shi ne kara yawan Bankoki da suke kan tsarin addinin musulunci domin kawo sauki ga al'umma da hakan ked a muhimmanci a rayuwar al'umma ta yau da kullum.

387476

captcha