Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Saphirnews cewa; kungiyoyin musulmi na jahar Limousin a kasar Faransa za su gudanar da taronsu na bai daya a karon farko a cikin wata Mayu mai kamawa. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan shi ne karon farko da kungiyoyin musulmi na wannan jaha za su gudanar da taronsu na bai daya, wanda zai hada da wasu kungiyoyin musulmin da ke cikin jahohin da ke kusa da su. Babbar manufar gudanar da wannan taro ita ce kara wayar da kan musulmi dangane da nauyin da ya rataya kansu wajen nuna wa sauran mutanen kasar manufofin addinin musulunci na gaskiya, sabanin farfagandar da ake yi kan musulunci da musulmi maras tushe a cikin Faransa da ma sauran kasashen yammacin turai.
388126