IQNA

Sakon Musulunci Yana Tattare Da Yafewa Da Kauna

15:16 - May 04, 2009
Lambar Labari: 1773854
Bangaren kasa da kasa: addinin musulunci yana dauke da sakon yafewa da kaunar juna a tsakanin al'umma day an uwantaka da kyawawan halaye da gujewa rarrabuwa da adawa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran bayan ta nakalto daga kamfanin dillancin labarai na Saudiya Spa ta watsa rahoton cewa: Muhammad Ahmadi Sani shugaban kungiyar hadin kan musulmi ya bayyana cewa: a taron da aka gudanar kan musulunci da kare muhalli ya yi bayani kan cewa: addinin musulunci ya koyar dam u son juna da kauna da kyautata ma'amala a tsakani da kuma aikata alheri da kiyaye hakkokin kowa da komi .kuma haka koyarwa ta addinin musulunci take a ko'ina a duniya.

398585


captcha