IQNA

Mambobin Kwamitin Bincike Na Majalisar Dinkin Duniya Sun Isa Gaza

15:59 - May 10, 2009
Lambar Labari: 1776508
Bangaren kasa da kasa: Mambobin kwamitin bincike da majalisar dinkin duniya ta kafa domin gani hakikanin abin day a faru a Gaza a lokacin da Isra'ila ta kaddamar da yaki kan yankin sun isa wasu yankunan zirin Gaza domin gane wa idanunsu gaskiyar lamarin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Khalee Times cewa; Mambobin kwamitin bincike da majalisar dinkin duniya ta kafa domin gani hakikanin abin day a faru a Gaza a lokacin da Isra'ila ta kaddamar da yaki kan yankin sun isa wasu yankunan zirin Gaza domin gane wa idanunsu gaskiyar lamarin. Kwamitin ya kunshi kwararru kan ayyukan yaki, da suka hada da tsohon alkalin kotun manyan laifuka ta majalisar dinkin duniya Richard Goldston, wanda kuma shi ne ke jagorantar kwamitin. A wata ganawa da ya yi da manema labarai ya bayyana cewa za su gudanar da ayyukansu na bincike a yankunan zirin Gaza da kuma yankunan Isra'ila, domin ganewa idanunsu hakikanin abin da ya faru a lokacin yakin da Isra'ila ta kaddamar kan zirin Gaza, ya kuma kirayi Isra'ila da ta ba su goyon baya kamar yadda ya kamata.

402032


captcha