Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridarTunisian online cewa; yan haka dai an fara gudanar da baje kolin hotuna da akayyakin fasahar musulunci a birnin Kirwan na kasar Tunisia, wanda za a kwashe makonni biyu ana gudanarwa. Daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu har da hotunan tsoffin masalattai na tarihi da wuraren ibada na birnin masu dogon tarihi. Wannan baje koli dai an zabi birnin Kirwan ne domin gudanar da shi, kasantuwar birnin shi ne aka zaba a matsayin babban birnin al'adun musulunci na shekara ta 2009, wanda kuma ko shakka babu birnin Kirwan birnin ne day a shahara da manyan malamai a tsawon tarihin musulunci, wadanda suka yi rubuce-rubuce a fagage daban-daban na ilmomin addinin musulunci.
402681